Miura mai sheakara 48 ya ki ritaya daga tamaula

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kazuyoshi ya fara murza leda tun yana da shekara 15 a Brazil

Dan kasar Japan, Kazuyoshi Miura, ya tsawaita zamansa a kungiyar Yokohama zuwa kakar wasa daya yana da shekara 48 da haihuwa.

Kazuyoshi wanda yake taka leda kusan kimanin shekaru 30, ya fara buga tamaula a kungiyar Santos ta Brazil a shekara 1986.

Tsohon dan kwallon tawagar Japan wanda ya fara yi mata wasanni a shekarar ta 2000 ya buga mata wasanni 89 jumulla inda ya ci kwallaye 55.

Ya fara wasa tun yana da shekara 15 a Brazil, kuma shi ne dan kwallon kafar da ya fi tsufa yana taka leda a duniya.

A makon jiya tsohon dan kwallon Ingila, Teddy Sheringham, ya yi wa kansa rijistar buga wasa a kungiyar da yake horas wa Stevenage yana da shekara 49 da haihuwa.