Kaka ya dawo buga wa tawagar Brazil kwallo

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Argentina ce za ta karbi bakuncin Brazil a ranar 13 ga watan Nuwamba

Dan wasan Barcelona, Neymar, ya kammala dakatarwar da aka yi masa daga buga wa Brazil tamaula, zai kuma fuskanci karawar da za su yi da Argentina.

Argentina ce za ta karbi bakuncin wasan neman tikitin shiga gasar cin kofin duniya da za su kara a ranar 13 ga watan Nuwamba.

An hukunta Neymar ne inda aka hana shi buga wasanni hudu, bayan da aka tashi daga gasar Copa America a karawar da Colombia ta ci Brazil daya mai ban haushi, sai ya buga kwallo ta bugi jikin Pablo Armero na Colombia.

Hakan ya sa bai buga sauran wasannin Brazil ba har zuwa wasan daf da na karshe da karawar da ta yi da Chile da kuma Venezuela a wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya.

Neymar zai buga a karawar da Brazil za ta yi da Argentina tare da Kaka wanda aka gayyato shi tawagar a farkon shekarar nan.

Argentina tana fama da 'yan wasanta da suke yin jinyar rauni da suka hada da Lionel Messi da Sergio Aguero da kuma Carlos Tevez.

Shi ma dan kwallon da yake murza leda a Paris St-Germain, Javier Pastore watakila ba zai buga wa Argentina wasan da za ta yi da Brazil din ba.