Sterling ya daura damarar cin kwallaye

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption A ranar Juma'a Ingila za ta buga wasan sada zumunta da Spain da kuma Faransa

Dan kwallon tawagar Ingila mai taka-leda a Manchester City, Raheem Sterling, ya daura aniyar ci wa kasarsa da kungiyarsa kwallaye da dama.

Sterling ya ci kwallaye 12 a kakar bara, a bana kuwa ya zura bakwai a raga tun daga lokacin da ya koma Manchester City daga Liverpool kan kudi fam miliyan 44.

Dan kwallon ya ci wa Ingila kwallaye biyu da kuma karin 29 da ya ci wa Liverpool da kuma Manchester City.

Ingila za ta kara a wasan sada zumunta da Spain a ranar Juma'a, sannan ta fafata da Faransa kwanaki hudu bayan nan.

'Yan wasan Ingila da dama na jinyar rauni kuma biyar ne daga cikin wadanda aka gayyato su 22 wasan sada zumuntar suka dara Sterling yawan buga wa Ingila wasanni.