Zan buga wa Ivory Coast tamaula - Toure

Image caption Rabon da Toure ya buga wa Ivory Coast tamaula tun a cikin watan Fabrairu

Yaya Toure ya ce zai cigaba da buga wa tawagar kwallon kafar Ivory Coast tamaula da zarar lokacin ya yi.

Rabon da Toure mai taka-leda a Manchester City ya buga wa kasarsa kwallo tun lokacin da aka kammala gasar cin kofin nahiyar Afirka da suka dauka a Fabrairu.

Haka kuma dan kwallon ba zai buga karawar da Ivory Coast za ta yi gida da waje da Liberia ba a wasannin neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya.

Dan wasan ya ce zai dawo murza wa kasarsa kwallo da zarar lokacin ya yi, kuma ya ce makomarsa na tawagar ta Ivory Coast, idan lokacin ya yi kowa zai sani.

Liberia za ta karbi bakuncin Ivory Coast a ranar 13 ga watan Nuwamba, sannan su buga wasa na biyu a ranar 17 ga watan Nuwamba.