'Na fito da Faransa a taswirar duniya'

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ibrahimovic ya zura wakulob din sa na PSG kwallaye 115 a raga.

Dan wasan gaba, Zlatan Ibrahimovic ya ce ficen da ya yi wurin murza leda ne a kulob din sa PSG, ya taimakawa kasar Faransa samun fice a duniya, inda ya yi nasarar zura kwallaye 115 a raga.

Dan kwallon mai shekaru 34, ya ci kwallaye 59 a wasanni 109 da ya buga wa kasar Sweden.

Ibrahimovic na shirin murza leda a wasan share fage domin neman cancantar buga gasar kwallon kasashen Turai inda kasarsa Sweden za ta fafata da Denmark a ranar Asabar.

"Zan so in buga a gasar zakarun Turai a Faransa," In ji Ibrahimovic.

Ya kara da cewa "Na shekara hudu ina buga wasanni a Sweden. Na kuma fito da taswirar ta a duniya, saboda haka ya kamata in sanya ta Faransa ma."

Sweden za ta karbi bakuncin Denmark a wasan farko da za a fara ranar Asabar, bayan haka kuma za a buga na biyu ranar 17 ga watan Nuwamba.