Bayanai kan Andre Ayew

Hakkin mallakar hoto getty
Image caption Ayew ya lashe wannan kyautar a 2013 lokacin yana murza leda a Marseille

Da kyar ne dan wasa ke iya sabawa da gasar Premier, amma dan kwallon Ghana, Andre Ayew nan da nan ya kwantar da hankali a wasannin da yake buga wa Swansea City tun lokacin da ya koma can da taka leda.

A wasan farko da ya buga a gasar bana, dan wasan ya ci Chelsea a Stamford Bridge a karawar da Swansea ta tashi 2-2 a gasar Premier.

Haka kuma ya ci kwallo a wasan farko da ya fara buga wa a filin Swansea a fafatawar da suka doke Manchester United 2-1 a daf da karshen watan Agusta.

Dan wasan mai shekaru 25, shi ne ya farke kwallon da United ta zura musu, daga baya ya bai wa Bafetimbi Gomis tamaula a bugun da ya yi masa da kafar hagu da suka ci United a kwallon da ya taimaka.

Cikin kankanin lokaci Ayew wanda ya kware da cin kwallaye da kai, ya lashe kyautar dan wasan da ya fi yin fice a gasar Premier ta watan Agusta, aka kuma yabe shi a matsayin daya daga cikin 'yan wasan da aka sayo a mai amfani.

Wani kuma abin mamaki shi ne Swansea ta saye shi a matakin dan kwallon da bashi da kwantiragi da wata kungiyar.

Ayew dan gidan tsohon zakaran kwallon kafa Abedi Pele yana da kwarewa da dabarun kwallon kafa da hakan ya sa ya dace da buga gasar Premier da tun farko ya ci ace yana buga ta.

Ayew ya shaidawa BBC cewar "Wannan shi ne lokacin da ya dace na buga gasar Premier domin na cimma mafarkina"

"Na kuma fuskanci gasar ne saboda naje Swansea a kan kari, dani aka yi wasannin atisayen tunkarar gasar Premier, na kuma san 'yan wasan wadanda suka dunga karamin kwarain gwiwa da bani damarmaki."

Ta yaya ya maida martani da cin kwallaye biyar da taimakawa a ci daya a wasanni 11 da ya buga a gasar Premier.

Ya je Ingila bayan da kakar wasa da ya yi a Marseille ta zama abin takaici da kunya yadda suka kammala a mataki na hudu a kan teburin gasar aka kuma fitar da su da wuri a kasar kofunan kasar.

Amma Ayew ya haskaka a kungiyar, yadda ya kaware da nuna fasaha da jajircewa ya sa aka karramashi a kungiyar da ya fara buga wa tamaula tun yana matashi, ya kuma yi shekaru 11 da ita ya dauki League Cup guda biya ya kuma ci kwallaye 61. Za ku iya zabe a na

Lokacin da yake ban kwana da magoya bayan kungiyar a watan Mayu a filin wasa bai san lokacin da ya barke da kuka ba a lokacin da wani sashi na filin ya dunga kiran sunansa.

Ba kuma shi ne karo na farko da dan kwallon ke sharbar kuka ba a cikin filin wasan tamaula.

A watan Fabarairu sai da aka ta rarrashinsa bayan da Ghana ta yi rashin nasarar lashe kofin nahiyar Afirka, bayan da suka barar da damar daukar kofin da rabonsu da shi tun shekaru 33 da suka wuce a inda Ivory Coast ta dauki kofin daga bugun fenariti.

Ayew ya ci kwallon da ya buga a bugun fenaritin kuma yana cikin 'yan wasan da suka yi kan-kan-kan a yawan cin kwallaye a gasar, a inda yake cikin 'yan wasa biyar da suka ci kwallaye uku.

Wasu kwallayen da ya ci suna da mahimmaci musamman wacce ya ci Afirka ta Kudu a minti na 83 da hakan ya kai Ghana da jan ragamar rukunin da suke ciki a gasar ta kofin Afirka.

Shin ko Ayew wanda ya lashe kyautar ta BBC a shekarar 2011 zai zama dan kasar Ghana na farko da zai lashe kyauta sau biyu?

Abin da masana ke cewa - Michael Oti Adjei, BBC Sport, Accra:

Babu tantamar cewar Andre Ayew ne dan kwallon kasar Ghana da ya fi farinjini, wanda ya fi fice a shekarar 2015 kuma wanda ya dara kowa a nahiyar Afirka, wanda hakan ne ake ganin zai iya zama dan kwallon kafar da zai sake lashe kayautar BBC.

Bisa yadda yake kan ganiyarsa a Ghana da kuma sabuwar kungiyarsa Swansea City ya kamata ya lashe kyautar. Ya taka rawa a gasar cin kofin nahiyar Afirka da Ivory Coast ta doke su a cikin watan Fabrairu a inda ya jagoranci Ghana ya kuma ci kwallaye da ya taimakawa kasar ta haskaka a gasar.

A kungiyar kuwa, ya kara kwazo matuka a gasar Premier da yake yi a inda ya ci kwallaye biyar daga wasannin 11 da ya yi a Swansea da kwallon da ya bayar aka ci Manchester United ta kara haskaka kwarewar da yake da ita a shekaran nan.