Bayanai kan Pierre-Emerick Aubameyang

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Karo na uku a jere Aubameyang na shiga cikin takara

Pierre-Emerick Aubameyang, dan kasar Gabon mai murza leda a Borussia Dortmund ya yi abin mamaki a bana, inda ya ci kwallaye da dama sannan ya kafa tarihin cin kwallaye a gasar Jamus da kuma yin bajintar da tsoffin 'yan wasan baya da suka yi.

An fara kakar wasan Jamus ta Bundesliga a shekarar 1963, a lokacin ne aka samu fitattun 'yan wasa da suka kware a yawan cin kwallaye da suka hada da Gerd Müller da Jupp Heynckes da kuma Karl-Heinz Rummenigge wanda suka dauki tsawon shekaru suna haskakawa, za ka bukaci kwarewa ta musamman kafin ka kafa tarihin cin kwallaye a Jamus.

Hakan kuma dan kwallon Gabon din ya yi, a inda ya ci kwallo a dukkan wasanni takwas da ya yi a jere a gasar a bana, ya dara tarihin da aka kafa da wasa biyu.

Lokacin da dan wasan ya ci kwallaye daga cikin wadanda suka ci Bayern Munich 5-1 a farkon watan Oktoba, nan ma ya kara kafa wani tarihin.

Kamar yadda ya ci kwallaye a wasanni biyu baya a kakar wasan 2014-15, wanda hakan ya sa ya ci kwallaye a kowanne wasa 10 da ya buga a gasar Bundesliga, tarihin da dan kwallon Cologne Klaus Allofs ya kafa shekaru 30 da suka wuce.

Aubameyang ya shaida wa BBC Sport cewa, mahaifinsa Pierre, tsohon dan kwallon Gabon ya taba sanar da shi cewar zai iya cin kwallo a kowanne wasa idan har yana son yin hakan.

"Amma hakan yana bukatar natsuwa kuma abinda nake maida hankali akai kenan."

In banda karawar da suka buga canjaras a inda ya bayar da kwallo sau biyu ga abokin wasa bayan tarihin da ya kafa daga nan ne Aubameyang dan kwallon Gabon da ya fara buga gasar Bundeslia ya mayar da martanin da ya zamo masa shekarar da ya fi haskakawa.

A wasanni biyu da ya yi na baga a gasar Bundesliga da ta Turai ya ci kwallaye uku sau biyu a wasa. Za ku iya zabe a nan

Yadda ya kware a iya cin kwallo ne ya sa 'auba' ke haskakawa a inda ya ci wa Dortmund kwallaye 20 a wasanni 17 da ya yi a gasar 2015-16.

Dortmund ba za ta taba mancewa da kakar wasan shekarar 2014-15 ba, a inda suka kammala gasar a mataki na bakwai duk da kasa fara taka rawar gani a gasar, amma kwazon da Aubameyang ya yi ne yasa dan wasan ya kare a matakin wanda ya fi yawan cin kwallaye a kungiyar, a inda ya ci 16.

Haka kuma ya ci kwallaye biyar a gasar cin kofin kalubale watau DFB Pokal, ciki har da wacce ya ci a wasan daf da na kusa da karshe da kuma wacce ya ci Bayern a wasan daf da karshe da ma wacce ya zura a wasan karshe da Wolfsburg ta lashe kofin.

Saboda haka ba wani abin mamaki bane da Aubameyang wanda Dortmund ta dauko daga St Etienne a shekarar 2013 da manyan kungiyoyin kwallon kafar Turai ke zawarcinsa. http://www.bvb.de/eng/News/Overview/Pierre-Emerick-Aubameyang-extends-BVB-contract-until-2020), kuma a cikin sauri aka tsawaita zamansa da zai ci gaba da murza leda zuwa Yunin 2020.

Yayin da kungiyarsa ke taka ranar gani, Aubameyang ba zai manta da gasar cin kofin nahiyar Afirka duk da cewar kyaftin kasar Gabon kwallaye biyu kacal ya ci a gasar da aka yi a Equatorial Guinea.

Kuma ya ci kwallayen ne a karawar da suka doke Burkina Faso 2-0, daga nan ne kuma suka yi rashin nasara a wasanni biyu da suka buga na gaba da hakan ya sa aka fitar da su daga gasar.

Wannan shi ne karo na uku da Aubameyang tsohon dan kwallaon AC Milan da tawagar matasan Faransa ke shiga cikin 'yan takarar gwarzon dan kwallon kafar da BBC ke karramawa.

Abin da masana ke cewa - John Bennett, BBC World Service:

"Yana da zafi amma baya iya cin kwallo" abind a masu sukar Pierre-Emerick Aubameyang ke cewa kenan, amma a wannan shekarar ya karyata batun da suke yi a kansa.

Akwai lokacin da ya fi kayatarwa - kamar cin kwallaye uku a wasa daya- amma yadda dan wasan Gabon din ya dinga cinsu a wasa akai-akai ya kara kai shi kololuwar tamaula. A kakar bana in banda dan kwallon Bayern Munich Robert Lewandwoski to da babu wanda zai yi takara da shi.

Wani karin abin Aubameyang yakan yi murmushi a koda yaushe da yin murnar cin kwallaye a bara. Kar mu shashance cewa dan wasan ya tashi tukuru ne da ya sa yake cin kwallaye a koda yaushe, ya kuma saurari masu sukarsa kan abinda suke cewa a kansa a koda yaushe.

Mahaifin Pierre na daya daga cikin wadanda suka bashi kwarin gwiwa da ya dunga umartarsa da ya tashi tsaye, babu wani dan Afirka da zai iya kwatanta kansa da bajintar da Aubameyang ya yi ba, kuma hakan ma yanzu ya fara.