United Ronaldo ya kamata ya dawo kwallo - Beckham

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sau uku Ronaldo yana lashe kyautar dan kwallon da ya fi yin fice a duniya

David Beckham ya bai wa Cristiano Ronaldo shawara cewar Manchester United ya kamata ya dawo da murza leda idan har zai bar Real Madrid.

Ronaldo ne ya gaji rigar Beckham mai lamba bakwai a lokacin da tsohon dan wasan tawagar Ingila ya koma Real Madrid da taka-leda a shekarar 2003.

Ronaldo mai shekaru 30 wanda ya lashe kyautar Balon D'Or karo na uku a bara, ya koma Real Madrid kan kudi £80m a shekarar 2009, kuma sai a shekarar 2018 yarjejeniyarsa za ta kare.

Beckham ya ce idan har Ronaldo ya yanke shawarar barin Real Madrid to babu shakka Manchester United ya kamata ya koma da murza leda.

Beckham ya buga wa United wasanni 394 a inda ya ci kwallaye 85 a shekaru 11 da ya yi a Old Trafford.