An soke wasu wasannin da za a yi a Faransa

Image caption Mutane 128 ne suka mutu a hare-haren da aka kai Faransa a ranar Juma'a

An soke wasu wasannin da za a yi a kasar Faransa, bayan da aka kai wasu hare-hare a Paris a inda aka kashe mutane 128.

'Yan kunar bakin wake uku ne suka mutu a lokacin da wasu bam suka tashi a kusa da babban filin wasan kasar Faransa a lokacin da take buga wasan sada zumunta da Jamus a ranar Juma'a.

Fashewar bama-bayam ya auku ne tun farkon fara wasan, a inda 'yan kallo suka kasa barin filin bayan da aka tashi, kuma wasu da dama suka koma tsakiyar filin wasan.

An dakatar da dukkan wasannin da aka shirya buga wa a wannan makon da suka hada da wasan kwallon zari ruga da kuma gasar cin kofin Kalubalen kasar.

Ga jerin wasannin da aka dakatar a Faransa.

Kwallon zari ruga:

  • Racing 92 vs Glasgow.
  • Oyonnax vs Ulster
  • Pau v Castres Olympique,
  • Bordeaux-Begles v ASM Clermont Auvergne,
  • RC Toulon v Bath

Kwallon kafa:

  • Wasanni hudu na kofin kalubale
  • Wasannin matasa da kuma na mata

Kwallon Volleyball:

  • Wasannin Ligue A
  • Wasanni hudu na mata 'yan rukuni na daya

Kwallon Hannu:

Wasa daya na 'yan rukuni na daya

Wasan Taekwondo:

Wasan gasar cin kofin Paris international.