Gwarzon dan kwallon Afrika na BBC a 2015

An bayyana sunayen 'yan kwallon kafa biyar da za a zabo wanda BBC za a karrama a matsayin gwarzon dan kwallon kafar Afirka a shekarar 2015.

An bayyana jerin sunayen ne a wani kasaitaccen buki da BBC ta shirya a kasar Afirka ta Kudu.

Cikin wadanda aka fitar har da dan kasar Algeria, Yacine Brahimi wanda ya lashe kyautar shekarar 2014, da Pierre-Emerick Aubameyang na Gabon, da dan wasan Ghana André Ayew, da na Senegal Sadio Mane da kuma Yaya Toure dan kwallon Ivory Coast.

Masu sha'awar kwallon kafar Afirka ne za su zabo wanda ya fi yin fice a fagen tamaula a nahiyar, a ranar 30 ga watan Nuwamba da karfe 1800 dai-dai da agogon GMT.

Za ku iya zabar wanda kuka ga ya dace ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa na BBC a bana ta wannan shafin;

LATSA NAN DOMIN ZABE

Ko kuma tura sako ta wannan lambar 44 7786 20 20 08:

  • Aika 1 domin zaben Pierre-Emerick Aubameyang
  • Aika 2 domin zaben André Ayew
  • Aika 3 domin zaben Yacine Brahimi
  • Aika 4 domin zaben Sadio Mané
  • Ko ka aika 5 domin zaben Yaya Toure

Farashin sakon dai-dai yake da wayar kira, tuntubi kamfaninka na sadarwa domin jin karin bayani.

Za a bayyana wanda zai lashe kyautar bana a ranar 11 ga watan Disamba tsakanin 1530-1600 agogon GMT a lokacin wani shiri na musamman a BBC World News da BBC World Service da kuma ta shafin Intanet na BBC Sport da kuma BBC Africa.

Uku daga cikin 'yan takarar bana da fitattun 'yan jaridu 46 da ke Afirka suka fitar sun taba lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa na Afirka na BBC da suka hada da Ayew wanda ya lashe a shekarar (2011) da Toure wanda ya dauka a (2013) da kuma Brahimi wanda aka karrama a (2014).

'Aubameyang'

Wannan ne karo na uku da Aubameyang ke shiga cikin 'yan takara, yayin da wannan ne karon farko da Mane ya shiga cikin wadanda ake sa ran za a zaba a gwarzon dan kwallon Afirka na bana.

Hakkin mallakar hoto getty
Image caption Aubameyang na cin kasuwa a Jamus

Aubameyang yana kan ganiyarsa ta cin kwallaye a kakar wasannin bana, bayan da ya yi na daya a matsayin wanda ya fi cin kwallaye a Borussia Dortmund a bara, da kafa tarihi a gasar kwallon Jamus ta bana.

Za ku iya zabe a nan

A watan Oktoba dan kwallon Gabon din mai shekaru 26, ya kafa tarihin dan wasa na farko da ya ci kwallaye a wasanni takwas a jere, kuma a karawa 17 da ya buga tamaula ya zazzaga kwallaye 20 a raga ciki har da cin kwallaye uku a wasa har sau biyu a jere.

'Ayew'

A wannan shekarar Ayew ya kai kololuwa a fagen tamaula, sai dai kuma komai na da iya ka matuka, A cikin watan Fabrairu dan wasan mai shekaru 25, ya fashe da kuka bayan da Ghana ta yi rashin nasarar lashe kofin nahiyar Afirka a hannun Ivory Coast.

Hakkin mallakar hoto getty
Image caption Ayew ya koma Swansea da kafar dama

Sai dai kuma dan wasan ya yi kan-kan-kan a matsayin wanda suka fi cin kwallaye a gasar kofin Afirkan, wanda hakan ya taimaka masa wajen cin kwallaye a gasar Premier a inda ya ci wa Swansea City kwallaye biyar daga wasanni 10 da ya buga mata. Za ku iya kada kuri'arku a nan

'Brahimi'

Brahimi mai taka leda a FC Porto ya nuna kansa da kwarewarsa a Afirka da nahiyar Turai, kuma dan kasar Algeria mai shekaru 25, ya ci gaba da zura kwallaye ta salon wasan da yake yi daga gefen fili ta gaba, a inda ya ci 13 a kakar wasan bara, sannan ya taimakawa FC Porto kai wa wasan daf da na kusa da karshe a karon farko wanda rabonta da hakan tun shekaru shida da suka wuce.

Hakkin mallakar hoto getty
Image caption Brahimi na kokarin kare kyautarsa

Dan wasan ya yi kaurin suna a gasar cin kofin zakarun Turai da iya salon taka leda daga gefen fili ta gaba da iya yanka wanda Eden Hazard na Chelsea da kuma dan wasan Barcelona Lionel Messi ne kadai suka sha gabansa a gasar. Ku jefa kuri'unku a nan

'Mane'

A ranar 16 ga watan Mayu, Mane dan kwallon Southampton ya ci kwallaye uku da aka fi zura su a raga cikin sauri a tarihin gasar Premier, wadanda ya ci su a cikin dakika 176 jumulla.

Hakkin mallakar hoto getty
Image caption Mane ya kafa tarihi a gasar Premier

Dan wasan ya kuma ci kwallaye 10 sannan ya taimaka aka ci biyar daga cikin wasanni 29 da ya buga a gasar Premier, kuma wannan kwazon da dan wasan mai shekatu 23 ya nuna ya sa aka maida shi mai wasan tsakiya, maimakon mai cin kwallo wato lamba tara. Za ku iya yin zabe a nan

'Toure'

Dan wasan da ya dauki kofi daga cikin 'yan takarar bana shi ne Yaya Toure, kuma shi ne wanda ya jagoranci kasarsa Ivory Coast da ta lashe kofin nahiyar Afirka karo na farko wanda rabonta da shi tun a shekarar 1992.

Hakkin mallakar hoto getty

Dan wasan mai taka leda a Manchester City ya taka rawar gani a kungiyar, wanda hakan ne ya sa hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa ta saka shi a cikin dan kwallon Afirka tal dake jerin 'yan takarar kyautar fitatcen dan wasan da ya fi yin fice a fagen tamaula a duniya wato kyautar Ballon d'Or. Za ku iya yin zabe a nan

Karin bayani