Kai Tsaye: Bayanai kan wasanni

Latsa nan domin sabunta shafin

Barkanmu da ziyarta shafin BBC Hausa kai tsaye a kan wasanni. Za mu kawo muku labarai kan wasanni da ke faruwa a Asabar musamman irin wainar da aketoyawa a nahiyar Turai dama duniya.

8:08 Wasannin karshe na cin kofin Firimiyar Nigeria mako na 38 Lahadi 15 Nuwamba

Hakkin mallakar hoto LMGNPFL Twitter
 • Heartland v El-Kanemi
 • Shooting Stars v Dolphins
 • Kwara Utd v FC Ifeanyiubah
 • Abia Warriors v Sharks
 • Wolves v FC Taraba
 • Sunshine Stars v Enyimba
 • Rangers v Bayelsa Utd
 • Akwa Utd v Lobi Stars
 • Wikki v Kano Pillars
 • Nasarawa Utd v Giwa FC

7:55 Wasan cike gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Turai Lahadi 15 ga watan Nuwamba

Hungary vs Norway

Wasannin neman tikitin shiga gasar cin kofin duniya nahiyar Afirka
Hakkin mallakar hoto Getty
 • Uganda vs Togo
 • Zambia vs Sudan
 • Janhuriyar Congo vs Burundi
 • Equatorial Guinea vs Morocco
 • Guinea vs Namibia

5:05 Kociyan tawagar matasa 'yan kasa da shekaru 23 na Nigeria, Samson Siasia, ya gayyaci 'yan wasan Nigeria hudu da suka lashe kofin duniya na matasa 'yan kasa da shekara 17 a Chile.

Hakkin mallakar hoto Thenff twitter

Siasia na shirye-shiryen zuwa gasar cin kofin matasa 'yan kasa da shekara 23 ta Afirka da Senegal za ta karbi bakunci. Latsa nan domin cigaba da karanta labarin.

4:25 Lewis Hamilton ne ke kan gaba a atisayen tunkarar gasar tseren motoci ta Brazilian Grand Prix duk da 'yar matsala da ya samu a tseren.

Hakkin mallakar hoto Getty

Hamilton matukin motar Mercedes ya yi na daya ne a atisayen a inda ya haura abokin takarrarsa Nico Rosberg shima matukin Mercedes da dakika 0.123.

Matukin Ferrari, Sebastian Vettel ne ya yi na uku sai Kimi Raikkonen ya kammala a mataki na hudu.

4:16 Yau ne za a buga wasan da za a tara kudi domin rabawa gajiyayyu a Old Trafford tsakanin Burtaniya da David Beckham zai jagoranci tawagar karkashin kociya Sir Alex Ferguson da kuma zakarun duniya da Carlo Ancelotti zai horas.

Hakkin mallakar hoto PA

Tuni aka tanadi tsaro domin kaucewa abinda ya faru a kasar Faransa:

'Yan wasan da za su buga wa Burtaniya:

David Beckham (kyaftin), David Seaman, David James, Jamie Carragher, Sol Campbell, Phil Neville, John Terry, Ashley Cole, Darren Fletcher, Nicky Butt, Trevor Sinclair, Paul Scholes, Gary McAllister, Ryan Giggs, Michael Owen, Peter Crouch, Alan Smith.

Fitattun 'yan wasan duniya:

World squad: Zinedine Zidane (kyaftin), Edwin van der Sar, Raimond van der Gouw, Cafu, Fernando Hierro, Fernando Couto, Mikael Silvestre, Maxwell, Luis Figo, Robert Pires, Christian Karembeu, Ji-sung Park, Clarence Seedorf, Patrick Vieira, Michael Ballack, Ronaldinho, Dwight Yorke, Ole Gunnar Solskjaer, Patrick Kluivert, Landon Donovan.

4:02 Muhawar da kuke tafkawa a BBC Hausa Facebook

Fatihu Yakubu Gulma: Babbar matsala a nan dai ita ce matsalar tsaro don a farkon gasar ne aka tsare tawagar Kano Pillars aka harbi wasu daga cikin manyan 'yan wasan kungiyar, kirana dai anan shi ne a kyautata tsaro kafin da kuma bayan wasannin.

Shaaibu Zidane: Shawarata ga kwallon kafar Najeriya ita ce ya kamata su rika gudanar da wasanninsu kamar yadda kasashen Turai suke gabatarwa ba nuna sonkai, ya zama ko kana gidanka za'a iya cinyeka wanda a yanzu bahaka bane shi yasa mafiya yawan mu yan Najeriya bamu damu da kallon wasan gida ba.

Sabo Muhammad Ture Karasuwa: Tabbas an samu chanje-chanje da dama, amma ina kira ga alkalan wasa a kan su kasance masu gaskiya da amana yayin da suke busa wasa.

Muawiyya Kazu: A gaskiya da sauran mu wajan alkalancin wasa, saboda har yanzu wai idan kungiya za ta karbi bakuncin wasa a gida sai tayi nasara, duk da ansami wasu kalililan da suka sami rashin nasara a gida, a ganina wajan alkalancin wasa da sauran gyara .

Usman Yahaya Mai Chelsea: Banga ci gaban da aka sami ba, don a matsayina na dan Nigeria ba zan iya kirgo 'yan wasan Nigerian Premier leage mutum 5 ba, amma zan iya kirgo England premier leage mutum 20. Ni banga ci gaba anan ba.

3:52 Damben gargajiya yana daga cikin wasannin Bahushe da ya dade yana yin shi.

Wannan takawa ce da aka yi tsakanin Garba Dan Malumfashi daga Arewa da Shagon Mada daga Kudu kuma turmi biyu suka yi a wata rana a gidan damben Ali Zuma dake Dei-Dei a Abuja Nigeria

3:47 A ranar Lahadi ce za a kare gasar Firimiyar Nigeria ta bana, bayan da aka buga wasannin mako 37.

Hakkin mallakar hoto npfl twitter

A ranar ce za a buga wasanni 10 a filaye daban-daban dake fadin kasar, wanda tuni Enyima ta lashe kofin banar kuma na bakwai da ta dauka jumulla. Latsa nan domin cigaba da karanta labarin.

3:21 Sakamakon wasannin neman tikitin shiga gasar kofin duniya nahiyar Afirka a ranar Juma'a 13 ga watan Nuwamba

Hakkin mallakar hoto the nff twitter
 • Madagascar 2 : 2 Senegal
 • Comoros 0 : 0 Ghana
 • Kenya 1 : 0 Cape Verde
 • Libya 1 : 0 Rwanda
 • Angola 1 : 3 South Africa
 • Niger 0 : 3 Cameroon
 • Liberia 0 : 1 Ivory Coast
 • Swaziland 0 : 0 Nigeria
 • Mauritania 1: 2 Tunisia

3:14 Sakamakon wasannin neman gurbi a gasar cin kofin duniya a Arewacin Amurka ranar Juma'a 13 ga watan Nuwamba

 • Guatemala 1 : 2 Trinidad And Tobago
 • Jamaica 0 : 2 Panama
 • Mexico 3 : 0 El Salvador
 • Costa Rica 1 : 0 Haiti
 • Canada 1 : 0 Honduras

3:02 An soke wasu wasannin da za a yi a kasar Faransa, bayan da aka kai wasu hare-hare a Paris a inda aka kashe mutane 128. Latsa nan domin cigaba da karanta labarin.

Hakkin mallakar hoto Getty

1:42 David Beckham ya bai wa Cristiano Ronaldo shawara cewar Manchester United ya kamata ya dawo da murza leda idan har zai bar Real Madrid. Latsa nan domin cigaba da karanta labarin.

1:36 Muhawar da kuke tafkawa a BBC Hausa Facebook

Dc Washington Mubi: A gaskiya wasannin bana ya yi kyau ganin yadda a baya za kaga in kulob yaje waje dakyar ya samu nasar, amma a bana ko kana gida ko kana waje za,a iya shanka.

Mudâssir Ibrâhim Ningi: A Gaskiya an sami chanji sosai a wannan gasar da'aka buga ta bana, Da fatan nan gaba za a samu canji wanda yafi wannan.

Engr Muhammad S Liman: A zahiri an samu cigaba sosai a fannin wannan gasar ta bana, ganin yadda ake iya cin kulob ko a rike shi canjaras a gida, ba karamin gyara aka samu ba, akasin da duk wacce ke gida ke da nasara.

El-Mukhtar Mohd: An sami cigaba idan aka duba yadda wasu kingiyoyin suka rika samun nasara a wasannin su na waje (away match)

Ibrahim Mohammed Damare: A gaskiya an samu cigaba amma ya kamata mahukutan firimiya ta nigeria su ringa kawo mana sharhin gasar a ridio ko a talabijin na kasar kai tsaye.

Nura Unguwar Bai Dambatta: Tabbas an samu canji sai dai ya kamata alkalai su gyara busa da suke yi.

12:57 Ingila ta yi rashin nasara a karon farko daga wasanni 16 da ta yi ba a doke ta ba a hannun Spaniya da ci 2-0 a karawar da suka yi a wasan sada zumunta a ranar Juma'a.

Hakkin mallakar hoto Reuters

Pérez Martínez ne ya fara cin Ingila a minti na 72, sannan Cazorla ya kara ta biyu saura minti shida a tashi daga wasan.

Tawagar Ingila ta samu tikitin shiga gasar cin kofin nahiyar Turai da za a yi a Faransa a shekarar 2016, kuma a wasannin da ta yi sai da ta lashe karawa 10 a jere kafin ta hadu da Spaniya.

12:35 A daren yau ne za a ci gaba da wasa tsakanin Argentina da Brazil a wasan neman tikitin shiga gasar cin kofin duniya da za su fafata a filin wasa na Estadio Antonio Vespucio Liberti.

Hakkin mallakar hoto Getty

Tun a daren Juma'a suka buga 1-1 amma rufan sama kamar da bakin kwarya da ya dunga zuba ya hana a karasa wasan. Kuma a karawar Argentina ce ta fara cin kwallo a minti na 34 da fara wasa ta hannun Ezequiel Lavezzi, yayin da aka dawo daga hutu ne Lucas Lima ya farke wa Brazil kwallon da aka zura mata.

A dai wasannin Kudancin Amurka Peru kuwa doke Paraguay ta yi da ci daya mai ban haushi.

12:15 Wasannin sada zumunta

Hong Kong vs Macau Portugal vs Russia

12:13 Wasannin neman tikitin shiga gasar cin kofin duniya na nahiyar Afirka, Asabar 14 ga watan Nuwamba

Hakkin mallakar hoto Getty
 • 2:00 Ethiopia vs Congo
 • 2:30 Tanzania vs Algeria
 • 5:00 Botswana vs Mali
 • 6:00 Gabon vs Mozambique

12:08 Wasannin cike gurbin gasar kofin zakarun Turai da za a yi Asabar 14 ga watan Nuwamba

Hakkin mallakar hoto Reuters
 • 6:00 Ukraine vs Slovenia
 • 8:45 Sweden vs Denmark

12:00 Wannan makon ake cigaba da buga wasannin neman tikitin shiga gasar cin kofin duniya da Rasha za ta karbi bakunci a shekarar 2018, da wasannin cike gurbi a gasar cin kofin nahiyar Turai da Faransa za ta karbi bakunci a shekarar 2016 da wasannin sada zumunta tsakanin kasashe da sauran wasannin da ake yi a wannan ranar da wadanda za a yi nan gaba da za mu kawo muku labaransu kai tsaye a wannan ranar.