Siasia ya gayyaci 'yan wasan U-17 hudu

Hakkin mallakar hoto Thenff twitter
Image caption Nwankali ne dan wasan da ya fi fice a gasar, Osimhen kuwa shi ya fi cin kwallaye a inda ya ci 10

Kociyan tawagar matasa 'yan kasa da shekaru 23 na Nigeria, Samson Siasia, ya gayyaci 'yan wasan Nigeria hudu da suka lashe kofin duniya na matasa 'yan kasa da shekara 17 a Chile.

Siasia na shirye-shiryen zuwa gasar cin kofin matasa 'yan kasa da shekara 23 ta Afirka da Senegal za ta karbi bakunci.

Cikin 'yan wasan da ya gayyata sun hada da kyaftin din tawagar Kelechi Nwakali da Victor Osimhen wanda da John Lazarus da kuma Udochukwu Anumudu.

Nwankali ne dan kwallon da ya fi yin fice a gasar, yayin da Osimhen ne wanda ya fi cin kwallaye a wasannin, a inda ya zura 10 a raga.

Tuni hukumar kwallon kafar Nigeria ta amince da goron gayyata da aka bai wa 'yan wasan hudu, ta kuma ba su hutun mako guda kafin su je sansanin horo da Nigeria ke yi a Gambia.

A wannan watan ne Nigeria ta lashe kofin matasa 'yan kasa da shekara 17 da aka kammala a Chile kuma karo na biyar da ta dauka a tarihi.