Ebola da Langa-Langa sun dambata a Dambe

Image caption Ebola da Langa-Langa a wannan takawar babu kisa

Turmi uku aka dambata tsakanin Ebola da Langa-Langa a wasan Lahadi da safe a gidan damben Ali Zuma dake Dei-Dei a Abuja, Nigeria.

Wasan ya kayatar yadda ya kamata ganin cewa Ebola dan wasan Kudu dogo ne kuma karfaffa, shi kuwa Aminu Langa-Langa daga Arewa bai kai Ebola tswo da jiki ba.

Amma kuma turmi uku suka taka babu kisa alkalin wasa Shagon Shagon Amadi ya raba wasan.

Shi ma wasan Aleka daga Kudu da Bahagon Balan Kada daga Arewa an biya 'yan kallo, illa dai fafatawar babu kisa a tsakaninsu.

Shi kuwa Bahagon Musan Kaduna daga Arewa kashe Dakakin Dakaka ya yi daga Arewa, Bahagon dai ya kuma kashe Garkuwan Dan Digiri daga Kudu a cikin kankanin lokaci.

Damben Nura Dan Karami daga Arewa da Shagon Dan Digiri babu kisa a turmi uku da suka yi, wasan Bahagon Musan Kaduna daga Arewa da Shagon Sikido shi ma babu kisa.

Sa zare ma tsakanin Shamsu Kanin Emi daga Arewa da Shagon Abata Mai daga Kudu turmi biyu suka yi babu wanda ya dafa kasa.