Ina takaicin kasa kokarin Chelsea - Fabregas

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Chelsea tana mataki na 16 a kan teburin Premier

Cesc Fabregas yana takaicin kasa taka rawar ganin da Chelsea ke yi a wasannin bana, kuma ya rasa me yake faruwa da kungiyar.

Chelsea mai rike da kofin Premier ta yi rashin nasara a wasanni bakwai daga guda 12 da ta buga a gasar, kuma tana mataki na 16 a kan teburi.

Fabregas ya fada a wata hira da ya yi da jaridar Marca ta Spaniya cewar sakamakon wasannin da suke yi ba ya yin daidai da kokarin da suke yi wa a wasannin.

Ya kara da cewar idan wasa yana yi da kai babu yadda ba za ka yi da kwallo ba, amma idan ba ya yi da dai duk yadda ka so ka yi da tamaula ba zai yi wu ba.

Fabregas, dan kwallon Spaniya, daya ne daga cikin 'yan wasan Chelsea da Jose Mourinho ya ce ba sa tabukawa a wasannin da suke yi.

Makonni biyu da suka wuce dan kwallon ya karyata rahoton da ke cewa suna kokarin yiwa Jose Mourinho zagon kasa.