Euro 2016: Faransa za ta karbi bakuncin gasar

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mutane 129 ne suka mutu 350 suka ji rauni a harin da aka kai wa Faransa a ranar Juma'a

Hukumar kwallon kafar nahiyar Turai Uefa, ta jaddada cewar za a buga wasan cin kofin nahiyar a Faransa a shekara mai zuwa kamar yadda aka tsara.

An yi tsammanin cewar watakila Faransa ba za ta karbi bakuncin wasannin ba sakamakon kai hari da aka yi a Paris inda mutane 129 suka mutu.

A wani jawabi da Uefa ta fitar a ranar Litinin ta ce tana aiki da jami'an Faransa domin tabbatar da cewar an samu tsaro a lokacin gasar da zai kai shekaru uku.

Ta kuma kara da cewar za su dauki matakan da suka dace domin ganin an gudanar da wasannin cikin kwanciyar hankali.

A ranar 12 ga watan Disamba ne za a raba jadawalin da kasashen za su fara gasar a Palais a Paris.

Za kuma a fara gudanar da gasar ne daga ranar 10 ga watan Yuni zuwa 10 ga watan Yulin 2016.