An nada alkalan gasar U-23 ba dan Nigeria

Hakkin mallakar hoto thenff
Image caption Senegal ce za ta karbi bakuncin gasar matasa 'yan kasa da shekara 23 ta Afirka

Hukumar kwallon kafa ta Afirka, Caf, ta nada alkalan wasan kwallon kafa da za su alkalanci gasar matasa 'yan kasa da shekara 23 ta Afirka da za a yi a Senegal.

Hukumar ta nada alkalai 10 da kuma wadanda za su taimaka musu a wasannin da za a fara a ranar 28 ga watan Nuwamba zuwa 12 ga watan Disamba.

Sai dai kuma Caf ba ta zabo alkalin wasan kwallon kafa daga Nigeria ba, wacce ta kammala gasar Firimiyar kasar a karshen makonnan.

Mai masaukin baki Senegal tana rukunin farko da ya kunshi Afirka ta Kudu da Tunisia da kuma Zambia, inda Algeria da Nigeria da Masar da kuma Mali suke rukuni na biyu.

Biranen Dakar da kuma M'Bour ne za su karbi bakuncin wasannin da za a fitar da kasashe ukun da za su wakilci Afirka a wasan kwallon kafa a gasar Olympics da za a yi a Brazil a 2016.

Ga jerin suanyen alkalan wasan gasar matasa 'yan kasa da shekaru 23:

 1. Redouane Jiyed Morocco
 2. Zio Juste Ephrem Burkina Faso
 3. Joshua Bondo Botswana
 4. Mehdi Abid Charef Algeria
 5. Hudu MunyemanaRwanda
 6. Antoine Max Depadoux Effa Essouma Cameroon
 7. Nampiandra Hamada Madagascar
 8. Sinko Bienvenu Cote d'Ivoire
 9. Diedhiou Malang Senegal
 10. Youssef Essrayri Tunisia

Mataimakan alkalan wasan kwallon kafar:

 1. Jerson dos Santos Angola
 2. Arsenio Marengula Mozambique
 3. Eldrick Adelaide Seychelles
 4. Drissa Kamory Niare Mali
 5. Berhe O. Michael Eritrea
 6. Yahaya Mahamadou Niger
 7. Mark Sonko Uganda
 8. Samba Malik Senegal
 9. Elmoiz Ali Mohamed Ahmed Sudan
 10. Mahmoud Ahmed Abo el Regal Egypt
 11. Issa Yaya Chad
 12. Oliver Safari Jamhuriyar Congo
 13. Sidiki Sidibe Guinea