An sace mahaifiyar Samson Siasia

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Siasia ke jan ragamar tawagar matasa 'yan kasa da shekaru 23

Hukumar kwallon kafar Nigeria ta bukaci masu garkuwa da mutane da su sako mahaifiyar Samson Siasia da aka sace a ranar Talata.

An sace Mrs Ogere Siasia a kauyen Odoni dake jihar Bayelsa, Nigeria, inda maharan suka je a kan babura uku suka farma gidan da take suka kuma dauke ta lokacin da take jinyar megidanta.

Siasia wanda zai ja ragamar tawagar matasa 'yan kasa da shekaru 23 zuwa gasar cin kofin matasa ta Afirka da za a yi a Senegal ya ce lamarin abin takaici ne yana kuma cikin damuwa.

Kociyan ya ce ya kamata a sako masa mahaifiyarsa domin ba shi da kudi, kuma abin da ya saka a gaba shi ne aikin bauta wa kasarsa da yake yi a yanzu.

Siasia ya tabbatar da aukuwar lamarin ya kuma ce tuni suka sanar da 'yan sanda domin su dauki matakin da ya dace.

A ranar 28 ga watan Nuwamba ce za a fara gasar wasannin neman gurbin kasashe uku da za su wakilci Afirka a wasan kwallon kafa a Olympics din da za a yi a Brazil a shekara mai zuwa.