Nigeria ta ci Swaziland 2-0

Hakkin mallakar hoto the nff twitter
Image caption Nigeria ta ci kwallayen biyu ne bayan da aka dawo daga hutun rabin lokaci

Tawagar Super Eagles ta kai wasan zagayen gaba a wasannin neman tikitin shiga gasar cin kofin duniya, bayan da ta doke ta Swaziland da ci 2-0 a ranar Talata.

Nigeria ta zura kwallon farko ta hannun Moses Simon daga bugun tazara, sannan ta ci ta biyun ta hannun Efe Ambros daf da za a tashi daga karawar da suka yi a Fatakwal.

Kasashen biyu sun tashi wasa ne canjaras a karawar farko da suka yi a Lobamba a ranar Juma'a.

Da wannan sakamakon Nigeria ta shiga jerin kasashe 20 da za su kai wasan zagaye gaban da za a raba su zuwa rukunnai biyar da za su kunshi kasashe biyar a kowanne rukuni.

Kasashe biyar ne za su wakilci nahiyar Afirka a gasar cin kofin duniyar da Rasha za ta karbi bakunci a shekarar 2018.