An samu kasashe 24 na gasar kofin Turai

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption A ranar Talata Ukraine ta samu tikitin shiga gasar da za a yi a Faransa a 2016

Ukraine ce kasa ta karshe da ta samu tikitin buga gasar cin kofin kwallon kafa na nahiyar Turai da za a buga a Faransa a 2016.

Ukraine din ta samu gurbin zuwa gasar ne bayan da ta buga canjaras da Slovenia wacce ta bakunta a ranar Talata. A fafatawar farko da suka yi Ukraine ce ta doke Sloveniya da ci 2-0.

Hakan ne ya kuma sa aka samu kasashe 23 da za su hadu da mai masaukin baki Faransa domin karawa a wasannin cin kofin nahiyar ta Turai.

A ranar 12 ga watan Disamba ne za a yi jadawalin da kasashen za su fara gasar a Palais da ke Paris.

Za kuma a fara gudanar da gasar ne daga ranar 10 ga watan Yuni zuwa 10 ga watan Yulin 2016.

Ga jerin kasashe 24 da zasu buga gasar cin kofin Turai:

Albania, Austria, Belgium, Croatia, Czech Republic, England, France, Germany, Hungary, Iceland, Italy, Northern Ireland, Poland, Portugal, Republic of Ireland, Romania, Russia, Slovakia, Spain, Sweden, Switzerland, Turkey, Ukraine, Wales.