Fifa ta yi watsi da daukaka karar Blatter da Platini

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption kwanaki 90 Fifa ta dakatar da Blatter da Platini daga shiga harkar kwallon kafa

Hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa, ta ki amince wa da daukaka karar da Sepp Blatter da Michel Platini suka shigar kan dakatar da su da aka yi.

A cikin watan Oktoba ne kwamitin ladabtarwa na hukumar ya dakatar da jami'an biyu daga shiga harkar wasannin tsawon kwanaki 90, kan zargin da ake yi musu na cin hanci a Fifa.

Ana zargin Blatter mai shekaru 79 da laifin saka hannu kan yarjejeniyar da ba za ta amfani Fifa ba, da kuma biyan Platini kudaden da ba sa bisa ka'ida saboda aikin da ya yi masa.

Dukkansu jami'an sun musanta zargin da ake yi musu za kuma su iya daukaka kara kan hukuncin da aka yanke musu a kotun daukaka karar wasanni ta duniya.

Shi ma Sakatare janar na Fifa, Jerome Valcke, yana daga cikin jami'an da aka dakatar a cikin watan na Oktoba, amma ba a ambace shi a rahoton da hukumar ta fitar a ranar Laraba ba.

Kafin a je hutun Kirsimeti ne kwamitin da'a na Fifa zai fara sauraren wadanda ake tuhuma da aikata ba dai-dai a hukumar.