Nasri ba zai koma wasa ba sai Febrairu

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Nasri ya bugawa City wasanni takwas a wannan kakar inda ya ci kwallo daya kacal a watan Agusta.

An kau da yiwuwar dan wasan tsakiya na Manchester City Samir Nasri ya shiga fili har sai nan da watan Febrairu saboda raunin da ya samu a jijiyar gwiwarsa.

Tun ranar 17 ga watan Oktoba ne dai rabon da Nasri dan shekaru 28 ya buga wa City wasa, lokacin da aka saka shi a rabin lokaci na biyu a wasan da suka doke Bournemouth 5-1.

Dan wasan mai buga wa kungiyar kwallon kafa ta kasar Faransa wasa ya saka hotonsa yana tafiya da sandunan guragu a shafinsa na Instagram.

A kasa ga hoton ya rubuta: ''Abin ba ya kashe ka karfi yakan kara maka. Zan sake dawowa da karfi fiye da a baya. Sai mun hadu nan da watanni uku.''

Karin bayani