Sturridge zai buga wasa da Man City - Klopp

Image caption Jurgen Klopp ya ce tunda Sturridge ya huta, zai iya buga wasa yanzu.

Kociyan Liverpool, Jurgen Klopp, ya ce yana sa ran dan wasan gaba Daniel Sturridge zai buga karawar da za su yi da Manchester City ranar Asabar.

Sturridge bai taba buga wasa karkashin jagorancin Klopp ba, kuma ya yi wasan mintuna 242 ne kacal a kasar gasar Premier ta bana.

Klopp ya ce, "Yanzu ya samu karfin jiki tunda ya huta sosai. Duk da cewa bai samu sauki dari bisa dari ba, za mu ga iyakar gudun ruwan sa".

Daniel Sturridge ya zura kwallaye 24 a Liverpool gabanin gasar Premier ta shekarun 2013 da 2014, bayan kuma ya dawo daga jinya, kwallaye shida kawai ya iya zurawa.