Sakamakon wasannin damben gargajiya

Image caption Bahagon Sarka daga Kudu da Cindo daga Arewa, babu kisa a wannan takawar da suka yi

An cigaba da fafatawa a wasanni da dama da aka yi da sanyin safiyar Lahadi a gidan damben Ali Zuma dake Dei-Dei a Abuja, Nigeria.

An fara yin damben ne tsakanin Dogon Na Manu daga Arewa da Garkuwan Mai Caji daga Kudu, a inda suka yi turmi biyu babu kisa aka raba wasan.

Wasan da aka yi na gaba kuwa Bahagon Ali Yaro ne daga Arewa ya doke Dogon Aleka a turmin farko kuma a dan kankanin lokaci.

Sa zare da aka yi tsakanin Fijot daga Arewa da Garkuwan Shagon Mada daga Kudu ta kayatar, sai dai babu wanda ya je kasa a turmi biyu da suka kara.

Wasan Autan Faya daga Kudu da Bahagon Ali Yara daga Arewa turmi daya kacal suka taka, inda aka kunburawa Autan Faya gefen idonsa na dama, shi yasa aka raba karawar.

Daga karshe ne aka rufe da damben da ya zo da takaddama tsakanin Shagon Musan Kaduna daga Arewa da Dogon Aleka daga Kudu.

Suna cikin dambatawa ne sai Dogon Aleka ya doki Shagon Musa ya kuma ta fi taga-taga kuma nan da nan shagon Musa ya mike ya doke Dogon Aleka har ya fadi kasa wan-war.

Daga nan ne wasu 'yan kallo suka ce Shagon Musa ya dafa kasa kafin ya doke Dogon Aleka wasu kuma suka ce bai dafa ba, da haka ne aka tashi daga wasan ba a zagaya da Shagon Musan Kaduna ba.