Coquelin na Arsenal zai yi jinyar makonni biyu

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption 'Yan wasan Arsenal da dama na yin jinya

Dan kwallon Arsenal, mai buga mata wasan tsakiya Francis Coquelin, zai yi jinyar makonni biyu, sakamakon raunin da ya ji a gwiwar kafarsa.

Coquelin, mai shekara 24, ya ji ciwo ne a karawar da West Brom ta ci Arsenal 2-1 a gasar Premier wasan mako na 13 a ranar Asabar a filin wasa na The Hawthorns.

Yan wasan Arsenal da dama na yin jinya da suka hada da Alex Oxlade-Chamberlain da Mikel Arteta da Jack Wilshere da Theo Walcott da kuma Danny Welbeck.

Kociyan Arsenal, Arsene Wenger, ya ce "suna da 'yan wasa da za su iya maye gurbin Coquelin kamar Mathieu Flamini da kuma Calum Chambers.

Gunners tana mataki na hudu a kan teburin Premier da maki 26, kuma za ta buga wasan mako na 14 ne a ranar Lahadi 29 ga watan Nuwamba da Norwich City.

Arsenal tana da maki uku a rukuni na shida a gasar cin kofin zakarun Turai za kuma ta kara da Dinamo Zagreb a ranar Talata.