Katongo ya sa Zambia ta shahara

Image caption Christopher Katongo ya fito da Zambia a idon duniya.

Burin masu sha'awar kwallon kafa a Zambia ya cika a lokacin da aka zabi dan kasar Christopher Katongo a matsayin zakaran kwallon kafar Afirka na BBC na shekarar 2012.

Kafin lokacin, shugaban kungiyar kwallon kafar kasar Kalusha Bwalya ne kadai dan Zambia da ya samu irin wannan kyautar.

Bwalya ya lashe gasar zakaran dan kwallon kafar Afirka na hukumar kula da kwallon kafar Afirka na shekarar 1988, sai dai babu wani dan wasan kasar da ya yi zarra a wasa tun bayan shi.

Don haka a lokacin da Katongo ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafar Afirka na BBC bayan ya jagoranci kungiyar Chipolopolo wajen daukar kofi, 'yan kasar Zambia sun ji dadi sosai.

Masu sha'awar kwallon kafa musamman sun ji dadi saboda jajiracewar da Katongo ya yi wajen ganin kungiyarsa ta yi nasara.

Masu sharhi da dama na ganin kyautar BBC da Katongo ya samu wata hanya ce ta zama gawutaccen dan wasa, wanda ya hada wsan kwallon kafa da aikin soji. Za ku iya yin zabe a nan

Hakan ya faru ne a lokacin da rundunar sojin Zambia ta kara masa girma.

Wani dan jarida mai sharhi a fagen wasanni, Ponga Liwewe, ya shaida wa BBC cewa, "kyautar gwarzon dan kwallon kafar Afirka na BBC da dan wasan ya samu ta kara masa daraja."

A lokacin da Katongo ya fara buga gasar cin kofin kwallon kafar Afirka a shekarar in 2006 da 2008, kungiyar Chipolopolo.

Sai dai shekaru biyu bayan hakan, Katongo ya sauya yadda 'yan kasar ke murza leda lamarin da ya sa Zambia ta kai matakin kwata fainal a karon farko a shekaru14.

Kazalika ya taka muhimmiyar rawa a a wasan karshe na gasar cin kofin Afirka ta shekarar 2012, wadda Gabon da Equatorial Guinea suka dauki nauyin gudanarwa.