An amince Benitez ya cigaba da horar da Madrid

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Magoya bayan Madrid sun ta rera wakar a sallami Benitez daga Bernabeu

Shugabannin Real Madrid sun amince da cewar Rafael Benite, ya cigaba da jan ragamar kungiyar, bayan wani taro da suka yi a ranar Litinin.

Tun a ranar Asabar Rafael Benite, ya fara fuskantar matsi, saboda doke su da ci 4-0 da Barcelona ta yi a gasar La Liga a Bernabeu.

A lokacin da ake wasan, magoya bayan Madrid sun yi ta rere wakar a sallami Benitez da kuma shugaban kungiyar Florentino Perez.

Ana sa ran Benitez, wanda ya horas da Liverpool da Chelsea, zai ci gaba da aikinsa, zai kuma jagoranci kungiyar wasan da Real za ta yi da Shakhtar Donetsk a gasar cin kofin Zakarun Turai da karawar da za su yi da Eibar a La Liga.

Shugaban Real Madrid, Florentino Perez ne ya bayar da sanarwar cewar sun amince da Benitez ya ci gaba da horas da kungiyar.

Tun da yammacin Litinin tsohon shugaban Madrid, Ramon Calderon ya ce ba ya tsammanin za a sallami Benitez.

Calderon ya ce bai kamata a dorawa kociyan laifi ba, matsalarsa ita ce ya zo ya maye gurbin Carlo Ancelotti wanda babu wanda ya san dalilin hakan.

"'Yan wasan suna goyon bayan Ancelotti a bara kafin a kore shi, amma dai Benitez yana iya kokarinsa".