Pirlo ba zai dawo Inter da wasa ba - Mancini

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Dan wasan ya buga wa Inter da AC Milan da Juventus

Kociyan Inter Milan, Roberto Mancini ya ce ba za su dauko Anrea Pirlo daga kulob din New York City, domin ya buga musu wasa aro ba.

Ana ta rade-radin cewar Pirlo mai shekara 36, zai sake komawa Inter ko kuma Manchester City da murza leda.

Tsohon dan wasan AC Milan da Juventus ya taba buga wa Inter Milan wasanni tun lokacin da ya zama kwararren dan wasan tamaula.

Pirlo ya buga wa New York City wasanni 13 tun lokacin da ya koma kulob din daga Juventus a tsakaiyar kakar wasannin Amurka.

Mancini ya ce shi bashi da lamabar Pirlo kuma a bakin 'yan jaridu yake jin labarin cewar zai dawo Inter da murza leda.