Blatter ba zai yarda da hukuncin FIFA ba

Hakkin mallakar hoto r
Image caption Sepp Blatter ya ce ya yi mamakin hukuncin da ake neman yanke wa Platini

BBC ta samu labarin cewa Sepp Blatter ba zai amince da hukuncin kwamitin da'a na FIFA ba, idan aka same shi da laifi.

Blatter dai na fuskantar yiwuwar haramta masa shiga harkar kwallon kafa na lokaci mai tsawo, amma abokansa sun shaida wa BBC cewa ya tsaya kai-da-fata cewa hukumomin kwallon kafa da ke karkashin FIFA su 209 ne kawai ke da hurumin sallamarsa daga harkar kwallo.

A watan Mayun bana ne aka zabi Blatter a karo na biyar a matsayin shugaban hukumar ta FIFA, amma bayan wani bincike da hukumomin Amurka da na Switzerland suka kaddamar, sai ya bayar da sanarwa cewa zai sauka daga mukamin ya kira sabon zabe.

A ranar 26 ga watan Fabrairun badi ake sa ran kada kuri'ar zaben sabon shugaba ga hukumar a Zurich.

A watan gobe ne kwamitin da'a na hukumar ta FIFA zai yanke hukunci a kan tuhume-tuhumen da ake yi wa Blatter da Michel Platini.