Za a yi wasan Afirka duk da harin Tunisia

Hakkin mallakar hoto caf
Image caption Kungiyar Orlando Pirates ta AFirka ta Kudu ta ce ta gamsu da shawarar da CAF ta yanke

Hukumar Kula da Kwallon Kafa ta Afirka, CAF, ta ce za a buga zagaye na biyu na wani wasan Gasar cin Kofin Zakarun Nahiyar Afirka, wato Confederation Cup, a Tunisia duk da harin da aka kai.

Kungiyar kwallon kafa ta Etoile du Sahel ce dai ake sa ran za ta karbi bakuncin Orlando Pirates ranar Lahadi a Sousse. Ranar Talata aka kai wani harin bam wanda ya hallaka mutane akalla 13 a Tunis, babban birnin kasar.

An kai hari a garin na Sousse ma a watan Yuni, inda aka kashe 'yan yawan bude ido 38.

Shugaban kasar ta Tunisia, Beji Caid Essebsi, ya ayyana dokar ta-baci ta kwanaki 30, yanzu haka kuma birnin Tunis na karkashin dokar hana fita.

Kungiyar ta Pirates ta ce duk abin da CAF ta yanke a kan lamarin ya yi daidai.

A zagaye na farko na wasan da aka buga ranar Asabar a Soweto ko wacce daga cikin kungiyoyin na da ci daya.

Karin bayani