Takarar FIFA: Champagne ya fara kamfe

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Jerome Champagne na da alaka da hukumomin kwallon kafa na Afirka

Daya daga cikin 'yan takarar shugabancin Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya, FIFA, ya gana da jami'an Majalisar Hukumomin Kwallon Kafa na Kasashen Tsakiya da Gabashin Afirka, CECAFA.

Bafarnshe Jerome Champagne na neman goyon baya ne don ya maye gurbin Sepp Blatter.

A da dai Mista Champagne jami'i ne a hukumar gudanarwar FIFA, kuma tun bayan saukarsa daga mukamin a shekarar 2010 ya kulla alaka da nahiyar Afirka.

A cewar Mista Champagne, shi ba bako ba ne ga hukumomin kwallon kafa na yankin:

"Na yi aiki da hukumomin kwallon kafar wannan yaki har tsawon shekaru 11", inji Mista Champagne, wanda ya kara da cewa, "Kuma bayan na bar hukumar zartarwar FIFA, na ci gaba da kulla alaka da su".

Dan takarar shugabancin hukumar ta FIFA ya kuma ce ba shahara ake bukata ga shugaban hukumar ba: "Na kan ji ana cewa ba ni da shahara ko kwarewa ko wadansu abubuwa, amma fa wannan harka ba abin da ya hada ta da shahara. Abin da ake bukata shi ne sanin kwallon kafa, da sanin halin da hukumomin kwallon kafa 209 na FIFA ke ciki, da sanin shugabanninsu da mataimakan shugabanninsu da sanin gasar da ake bugawa a kasashen da sanin kungiyoyin kwallon kafarsu", inji Mista Champagne.

Karin bayani