'Yan wasan Manchester basu da 'yanci'

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Rene Meulensteen ya ce 'yan wasan Manchester basu da 'yancikamar da.

Tsohon masu taimakawa kociyan Manchester Rene Meulensteen, ya ce 'yan wasan kulob din na fama da rashin 'yanci a karkashin jagorancin Louis van Gaal.

Dan kasar Jamus din ya kara da cewa alamu na nuna cewa 'yan kwallon ba su da damar sakin jiki kamar lokacin da Alex Ferguson yake shugabantarsu.

"Lamarin na da wuyar sha'ani" Meulensteen ya gaya wa BBC, yana mai cewa, "Akwai lokutan da 'yan wasa za su iya yin wasu dabaru amma sai ka ga sun ja da baya. Magoya bayan kulob din kuma sun ki jinin hakan".

Manchester da PSV Eindhoven sun tashi babu ci a karawar da suka yi ranar Laraba, hakan kuma na nufin sun zira kwallaye shida ke nan cikin wasanni takwas.