Manchester City ta dare kan teburin Premier

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption City za ta buga ne da Hull City a wasan mako na 15 a gasar Premier

Manchester City ta sake komawa kan teburin Premier, bayan da ta doke Southampton da ci 3-1 a gasar ta Premier da suka buga wasan mako na 14 a ranar Asabar.

City ta fara cin kwallo ta hannun De Bruyne a minti na 9 da fara tamaula sannan Delph ya kara ta biyu a minti na 20 da take wasa.

Bayan da aka dawo ne daga hutun rabin lokaci Southampton ta farke kwallo daya ta hannun Shane Long, Kolorov ya ci wa City kwallo ta uku saura minti 21 a tashi daga wasan.

Manchester City ta koma mataki na daya a kan teburin da maki 29 dai-dai dana Leicester wacce ta buga kunnen doki da Manchester United a ranar ta Asabar.

City za ta buga wasanta na gaba ne da Hull City, yayin da Southampton za ta kece raini da Liverpool.