Bale da Ronaldo sun ci wa Real Madrid kwallo

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Real Madrid tana mataki na uku a kan teburin La Liga

Real Madrid ta doke Eibar da ci 2-0 a gasar La Liga wasan mako na 13 da suka kara a ranar Lahadi.

Gareth Bale ne ya ci kwallon farko da ka daga bugun da Luca Modric ya yi yo masa kafin aje hutun rabin lokaci.

Madrid din ta kara ta biyu ta hannun Cristiano Ronaldo daga bugun fenariti, kuma kwallo ta 16 da ya ci kenan a bana.

Da wannan sakamakon Real Madrid ta hada maki 27 ta kuma koma mataki na uku a kan teburin La Liga.

Mahukuntan Real Madrid sun amince da cewar Rafael Benitez ya ci gaba da horar da kungiyar, bayan da ya sha matsi bisa doke su 4-0 har gida da Barcelona ta yi.