Rasha ta hana kungiyoyinta dauko dan kwallon Turkiya

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Rasha na son mayar da martani kan jirgin yakinta da Turkiya ta harbo

Za a dakatar da duk wata kungiyar kwallon kafa ta Rasha da ta dauko dan wasan kwallon kafa dan kasar Turkiya domin ya taka mata leda.

Rashin jituwa ta barke ne tsakanin kasashen biyu tun lokacin da Turkiya ta harbo jirgin saman Rasha a kan gabar kasar Syria, inda matukin jirgin ya mutu.

Ministan wasanni na Rasha, Vitaly Mutko ya sanarwa wata kafar yada labarai cewar tuni suka sanar da kungiyoyin kwallon kafar kasar dalilin da ya sa suka dauki matakin.

Sai dai kuma shugaban ya ce hukuncin ba zai shafi 'yan wasan da a yanzu haka suke murza leda da kungiyoyin Rasha ba.

Haka kuma ya kara da cewar kamfanonin da suke aikin gina filayen wasannin da za su karbi bakuncin gasar cin kofin duniya, za su ci gaba da aikinsu.

Dakatarwar ta shafi duk kungiyar dake son sayo yan wasan Turkiya da zarar an bude kasuwar saye da sayar da 'yan wasan kwallon kafa, amma duk wanda zai dauko dan wasa kafin lokacin hukunci ba zai shafe shi ba in ji Mutko.