Bilic ya damu da raunin da Sakho ya ji

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Bayan Sakho, Payet da Valencia suna yin jinya

Kociyan West Ham, Slaven Bilic, ya ce ya damu da raunin da Diafra Sakho ya ji a wasan da suka buga da West Brom ranar Lahadi.

Dan wasan ne da kansa ya nuna alamun a cire shi daga wasan sakamakon raunin da ya ji a karawar da suka tashi kunnen doki 1-1 da West Brom din.

Bilic ya ce "Na damu da raunin da dan wasan ya ji fiye da sakamakon wasan da muka samu, kuma yanzu ya yi wuri mu auna girman raunin da ya ji, amma ba zai wuce raunin tsoka ba".

Kociyan ya kara da cewar raunin da Sakho ya ji ya girgiza su, tunda zai yi jinya tare da Enner Valencia da kuma Dimitri Payet.

Payet yana yin jinyar watanni uku sakamakon raunin da ya ji a kafarsa tun farkon watan Nuwamba, yayin da

Shi kuwa Valencia ya fara yin jinya tun cikin watan Yuli ta raunin da ya ji a wasan neman gurbin shiga gasar Europa League.