Wenger ya fadi dalilin saka Sanchez a wasa

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Arsenal ta kara samun yawan 'yan wasanta da suke yin jinya

Kociyan Arsenal, Arsene Wenger, ya fadi dalilin da ya sa ya saka Alexis Sanchez a wasan Premier da suka tashi 1-1 da Norwich ranar Lahadi.

A karawar ce Sanchez da 'yan wasan Arsenal suka yi rauni, wanda hakan ya kara yawan 'yan wasan kungiyar dake yin jinya.

Wenger ya ce Sanchez ya dan bugu a karawar da Arsenal ta ci Dinamo Zagreb a Gasar cin Kofin Zakarun Turai 3-0, kuma Sanchez ne ya ci kwallaye biyu a wasan.

Kocin ya kara da cewar "Na shirya zan ajiye shi ya huta a wasanmu na Lahadi, amma Sanchez da kansa ya ce min zai iya buga karawar".

Dan wasan Arsenal, Santi Cazorla, ya karasa fafatawar ne da rauni a kafarsa, yayin da Laurent Koscielny ya gamu da buguwa a kugunsa.

Yan kwallon Arsenal dake yin jinya sun hada da Mikel Arteta da Tomas Rosicky da Jack Wilshere da Danny Welbeck da kuma Theo Walcott.