Chelsea ta mika bukatar fadada filin wasanta

Hakkin mallakar hoto Hammersmith and Fulham council
Image caption Chelsea ta fara buga tamaula a Stamford Bridge a 1905

Chelsea ta mika bukatar son fadada filin wasanta na Stamford Bridge, domin ya koma daukar 'yan kallo 60,000.

Chelsean tana son rushe filin wasan nata da yake daukar 'yan kallo 41,600 da kuma sauran gine-gine da ke harabarsa.

A wani sako da ta wallafa a shafinta na intanet, kungiyar ta ce idan ta kammala gina filin wasan zai samar da sabbin wuraren atisaye da kayayyaki da wuraren zaman kallo da za su kayatar.

Chelsea ta fara wasa a filin Stamford Bridge ne tun a shekarar 1905, kuma rabon da ta yi wa filin kwaskarima tun shekarar 1990.

Filin wasan na Chelsea bai kai girman filayen abokan hamayyarta a gasar Premier ba, kamar na Manchester United mai daukar 'yan kallo 76,000 da na Arsenal mai daukar 'yan kallo 60,000 da kuma na Manchester City mai daukar 'yan kallo 55,000.