Klopp ya karyata maganar neman sabon gola

Hakkin mallakar hoto epa
Image caption Liverpool tana mataki na shida a kan teburin Premier

Kociyan Liverpool, Jurgen Klopp ya karyata labarin da ake cewa yana neman mai tsaron raga domin maye gurbin Simon Mignolet.

A watan Janairun 2016 ne za a bude kasuwar saye da sayar da 'yan wasan tamaula, inda ake cewa Klopp zai sayo mai tsaron ragar Stoke City dan kasar Ingila Jack Butland.

Amma kuma kociyan ya karyata hakan yana mai cewa ya gamsu da yadda Mignolet ke gudanar da aikinsa a Liverpool.

Liverpool za ta ziyarci Southampton domin karawa a wasan daf da na kusa da karshe a League Cup a ranar Laraba.

Mignolet, dan kasar Belgium, wanda Brendan Rodgers ya daina saka shi a wasa a bara, ya buga wa Liverpool wasanni shida wanda kwallo ba ta shiga ragarsa ba, a bana.