Benzema ba shi da gurbi a Faransa - Manuel Valls

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption A shekara mai zuwa ne Faransa za ta karbi bakuncin wasannin cin kofin nahiyar Turai

Firayim Ministan Faransa, Manuel Valls, ya ce dan kwallon Real Madrid, Karim Benzema, ba shi da gurbin da zai buga wa tawagar kwallon kafar kasar.

Ana binciken Benzema da laifin kokarin bata wa abokin buga tamaularsa Mathieu Valbuena, sai dai ya karyata aikata ba daidai ba.

Dan kwallon mai shekaru 27, wanda ya ci wa Faransa kwallaye 27, zai fuskanci tuhuma kan shirya bata suna da ya shafi faifan bidiyo kan jima'i.

Valls ya fada a wata hira da wata kafar yada labarai ta Faransa da cewa "dan wasa abin koyi ne ga 'yan baya, idan bai da da'a kuwa, ba shi da gurbin wakiltar Faransa a wasanni".

Faransa ce za ta karbi bakuncin gasar cin kofin nahiyar Turai da za a yi shekara mai zuwa.