Cahill ya tsawaita zamansa a Chelsea

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Cahill zai ci gaba da buga tamaula a Stamford Bridge har zuwa karshen kakar 2019

Mai tsaron bayan Chelsea, Gary Cahill, ya saka hannu kan sabuwar yarjejeniyar ci gaba da buga wa Chelsea tamaula zuwa shekara hudu a Stamford Bridge.

Cahill, mai shekara 29, dan kwallon Ingila, ya buga wa Chelsea wasanni 177, tun lokacin da aka sayo shi daga Bolton kan kudi fam miliyon bakwai a watan Janairun 2012.

Dan kwallon ya kuma lashe kofin Premier da kofin zakarun Turai da FA Cup da kuma Europa League.

Kwantiragin da dan kwallon ya cimma yarjejeniya da Chelsea tun a baya, za ta kare ne a karshen kakar wasan bana.

A kakar wasan bana, Cahill ya buga wa Chelsea wasanni 10, wacce take mataki na 14 a kan teburin Premier.