An nada Gary Neville kociyan Valencia

Image caption Gare Neville zai cigaba da aiki tare da tawagar kwallon kafar Ingila

Valencia ta nada tsohon dan kwallon Manchester United, Garry Neville, a matsayin sabon kociyanta, wanda zai yi aiki zuwa karshen kakar wasan bana.

Gary, mai shekara 40, zai fara horas da Valencia tamaula a ranar Lahadi, kuma zai cigaba da aiki tare da tawagar kwallon kafar Ingila.

Mamallakin kungiyar Valencia, dan kasar Singapore, Peter Lim yana da ruwa da tsaki a kulob din Salford City da kuma wata kungiya da ba ta buga League wacce Neville suka yi hadakar mallaka.

Dan uwan Gary wato Phil wanda ya fara aikin mataimakin mai horas da Valencia a watan Yuni zai cigaba da gudanar da aikinsa na mataimakin kociya.

A ranar Laraba ce Valencia za ta karbi bakuncin Lyon a gasar cin kofin zakarun Turai, wanda shi ne wasan farko da Neville zai jagoranci kungiyar.