Nigeria ta shiga kungiyar gasar leagues ta duniya

Image caption A cikin watan Nuwamba aka kammala gasar Firimiyar Nigeria

Nigeria da Kenya da Afirka ta Kudu sun shiga rukunin gasar kwallon kafa ta kwarrarru, da nufin kafa kungiyar gasar kwallon kafa ta duniya, bayan wani taro da suka yi a Faransa.

Kasashen Afirkan uku sun shiga cikin jerin fitattun gasar kwallon kafa 20 na duniya da suka hada da gasar Premier Ingila da Spaniya da ta Faransa domin aiki tare da hukumar Fifa.

Shehu Dikko, shugaban hukumar gasar Firimiyar Nigeria ya ce yana da yakinin cewar kasahen za su amfana a nan gaba.

Dikko ya shaidawa BBC cewar an amince da cewar kashin bayan cigaban wasan tamaula ya ta'allaka ga gasar League ne.

Shugaban hukumar kwallon kafar Faransa, Frederic Thiriez, ya sanar da cewar sabuwar kungiyar da za a kafa za ta fara aiki a watan Janairun shekara mai zuwa.

Kuma kungiyar za ta kunshi mambobi daga gasar da ke da hukumar da ke gudanar da gasar kwallon kafa mai cin gashin kanta.