An sake kama manyan jami'an FIFA biyu

Hakkin mallakar hoto d
Image caption Ana zargin Alfredo Hawit da Juan Angel Napout da karbar na-goro

An kama wadansu mataimakan shugaban hukumar FIFA su biyu yayin wani samame da aka kai wani otal a Switzerland da sassafe a bisa zargin karbar rashawar da ta kai miliyoyin daloli.

An kama Alfredo Hawit, shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Arewaci da Tsakiyar Amurka da Caribbean, CONCACAF, da Juan Angel Napout, shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Kudancin Amurka, CONMEBOL, ne a otal din Baur au Lac da ke Zurich, inda a watan Mayu aka kama wadansu jami'an hukumar ta FIFA da dama.

Kwamitin zartarwa na FIFA dai na ganawa a birnin,don kada kuri'a a kan wadansu sauye-sauye a tsare-tsaren tafiyar da hukumar.

Ma'aikatar Shari'a ta Amurka ce ta bukaci a yi kamen a ci gaba da binciken da take yi a kan zargin aikata almundahana a hukumar ta FIFA.

A cewar Ma'aikatar Shari'a ta Switzerland, ana zargin Hawit da Napout ne da karbar na-goro yayin sayar da hakkin tallata gasar kwallon kafa a Latin Amurka da na wasannin neman tikitin shiga Gasar Kwallon Kafa ta Duniya.

Shugaban kwamitin yi wa FIFA kwaskwarima, Francois Carrard, ya shaida wa manema labarai a Zurich cewa kamen "wani muhimmin mataki ne" a yunkurin da ake yi na kawo sauyi "saboda FIFA ta samu damar kintsa kanta".

Karin bayani