FIFA ta amince da wadansu sauye-sauye

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shugaban kwamitin gyaran fuska ga FIFA, Francois Carrard, ya sanar da sauye-sauyen

Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya, FIFA, ta amince da wani jerin sauye-sauye da take fatan zai mayar da ita 'yar zamani, abar yarda, kuma mai tarin kwarewa nan da shekarar 2018.

A cikin sauye-sauyen har da karin yawan matan da ke rike da manyan mukamai, da kayyade wa'adin manyan jami'ai wadanda za a bayyana wa duniya albashin da suke dauka.

Wajibi ne hukumonin kwallon kafa da ke da wakilci a FIFA su 209 su rattaba hannu a kan wadannan shawarwari a watan Fabrairun badi kafin a fara aiki da su.

Sai dai kuma an jinkirta yanke shawara a kan yiwuwar kara yawan tawagogin da ke karawa a Gasar Kwallon Kafa ta Duniya har sai an kara yin nazari.

Wakilan FIFA daga Asiya da Afirka sun goyi bayan kara yawan tawagogin daga 32, kamar yadda ake samu tun daga 1998, zuwa 40.

Sai dai kuma wasu jami'an hukumar zartarwa ta FIFA sun hakikice cewa ana bukatar yin nazari mai zurfi a kan tasirin yin hakan kafin a amince da shawarar.

Karin bayani