Marcos Rojo ya gurde a kafada

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wasanni 11 Marcos Rojo ya buga wa Manchester United a kakar bana

Mai tsaron baya na kungiyar Manchester United, Marcos Rojo, na fuskantar yiwuwar dumama benci bayan da ya gurde a kafada yayin atisaye.

Lamarin dai ya faru ne ranar Laraba kuma a kafadar da Rojo ya taba gurdewa a kakar wasa ta bara yayin wasansu da Manchester City.

A wancan lokacin ba a yi wa dan wasan tiyata a kafadar ba, amma duk da haka sai da ya kwashe mako hudu ba ya buga wasa.

United ta ki cewa uffan a kan wannan lamari, amma mai yiwuwa kocin kungiyar, Louis van Gaal, ya yi bayani a kai yayin ganawarsa ta mako-mako da manema labarai ranar Juma'a.

Karin bayani