Kai Tsaye: Bayanai kan wasanni

Latsa nan domin sabunta shafin

Barkanmu da ziyartar shafin BBC Hausa kai tsaye a kan wasanni. Za mu kawo muku labarai kan wasanni da ke faruwa a ranar Asabar musamman irin wainar da ake toyawa a nahiyar Turai dama duniya.

Hakkin mallakar hoto AFP

8:15 Borussia Monchengladbach ta doke Bayern Munich da ci 3-1 a gasar Bundesligar Jamus da suka fafata a ranar Asabar. Latsa nan domin ci gaba da karanta labarin.

7:50 Sakamakon wasannin damben gargajiya na ranar Asabar da aka yi a gidan damben Ali Zuma dake Dei-Dei a Abuja Nigeria.

Shagon Caka-caka daga Arewa ya doke Shagon Ebola daga Kudu.

Sauran damben da aka yi babu kisa

 1. Mai Gaban Karo daga Kudu da Shagon Shukurana daga Arewa
 2. Shagon Buzu daga Arewa da Garkuwan Autan Faya daga Kudu
 3. Shagon Shagon 'Yar Tasa daga Arewa da Mai Gaban Karo daga Kudu
 4. Garkuwan Shagon Alabo daga Kudu da Fijot daga Arewa
 5. Dakakin Dakaka daga Kudu da Shagon Musan Kaduna daga Arewa
Hakkin mallakar hoto AP

4:41 Stoke City ta doke Manchester City da ci 2-0 a gasar Premier wasan mako na 15 da suka kara a filin wasa na Britannia ranar Asabar. Latsa nan domin ci gaba da karanta labarin.

2:53 Hukumar wasannin tsalle-tsalle da guje-guje ta duniya, The IAAF ta bude damar bai wa kasashen da ke da sha'war karban bakuncin wasanninta biyu na gaba da za ta yi, bayan da ta dagatar da Rasha shiga wasannin.

Hakkin mallakar hoto Getty

An dakatar da Rasha ne, bayan da aka samu hukumar da ke kula da shan kwayoyi masu kara kuzari a lokacin wasanni ta kasar da kau da kai ga 'yan wasan da suke ta'ammali da kwayoyin.

Tun farko an shirya cewar Rasha ce za ta karbi bakuncin World Race Walking Team Championships da kuma wasannin matasa a World Junior Championships in 2016.

Duk kasar da ke da sha'awar karbar bakuncin wasannin dole ne ta mika bukatar hakan kafin 7 ga watan Disamaba.

A kuma ranar 7 ga watan Janairu ne, The IAAF za ta bayyana kasar da za ta karbi bakuncin wasannin.

2:38 Wladimir Klitschko ya zabi ya sake yin dambe da Tyson Fury a 2016, bayan da ya yi rashin nasarar kumbunansa na damben boksin da suka kara a Dusseldorf a ranar Asabar.

Hakkin mallakar hoto epa

Tun kafin su kara a tsakaninsu da akwai yarjejeniyar duk wanda aka doke zai iya neman dambatawa a wasa na biyu

Fury, mai shekaru 27, ya kawo karshen rike kambunan da Klitschko dan kasar Ukraine ya rike na tsawon shekaru tara ba tare da an doke shi ba a damben boksin.

Fury ya lashe kambun WBA da IBF da kuma WBO daga hannun Klitschko, rabon da a doke shi tun a 2004, bayan da ya sha kashi a hannun Lamon Brewster. Tura wannan labarin Game da aika wa

Klitschko ya yi shekara 11 ba a doke shi ba a damben boksin, kuma sau 19 yana kare kambunansa kafin ya yi rashin nasara a hannun Fury.

Hakkin mallakar hoto AP

2:00 Zlatan Ibrahimovic ya zama dan wasan Paris St-Germain da yafi yawan ci wa kungiyar kwalllaye a gasar kasar Faransa ta Ligue 1. Latsa nan domin ci gaba da karanta labarin

Hakkin mallakar hoto Getty

1:55 Hukumar kwallon kafar Spaniya ta kori Real Madrid daga gasar Copa del Rey, sakamakon samunta da laifin saka dan wasan da bai dace ba a karawar da suka yi da Cadiz. Latsa nan domin ci gaba da karanta labarin

1:00 Stoke City vs Manchester City

Hakkin mallakar hoto Getty

'Yan wasan Stoke City: 01 Butland08 Johnson17 Shawcross26 Wollscheid03 Pieters06 Whelan20 Cameron22 Shaqiri14 Afellay10 Arnautovic27 Krkic

Masu jiran kar-ta-kwana: 11 Joselu12 Wilson15 Van Ginkel16 Adam18 Diouf19 Walters29 Haugaard

'Yan wasan Manchester City: 01 Hart03 Sagna26 Demichelis30 Otamendi11 Kolarov06 Fernando25 Fernandinho17 De Bruyne21 Silva07 Sterling14 Bony

Masu jiran kar-ta-kwana: 13 Caballero15 Jesús Navas18 Delph22 Clichy72 Iheanacho76 Garcia Alonso77 Humphreys-Grant

Alkalin wasa: Martin Atkinson

12:56 African U23 Championship 2015 wasan karshe na rukunin B

Hakkin mallakar hoto theNFF Twitter
 • 6:00 Masar vs Mali
 • 6:00 Algeria vs Nigeria
Hakkin mallakar hoto AP

12:45 Holland Eredivisie League wasannin mako na 15

 • 6:30 SBV Excelsior vs FC Twente Enschede
 • 7:45 De Graafschap vs FC Utrecht
 • 7:45 Vitesse Arnhem vs PSV Eindhoven
 • 8:45 Ajax Amsterdam vs SC Heerenveen
Hakkin mallakar hoto GOOGLE

Portugal SuperLiga wasannin mako na 15

 • 5:15 Os Belenenses vs Vitoria Setubal
 • 7:30 FC Porto vs Pacos De Ferreira
 • 9:45 CS Maritimo vs Sporting CP

Belgium Jupiler League wasannin mako na 18

 • 6:00 KV Oostende vs Sint-Truidense VV
 • 8:00 Mouscron Peruwelz vs KV Mechelen
 • 8:00 OH Leuven vs KVC Westerlo
 • 8:30 Waasland-Beveren vs Standard de Liege
Hakkin mallakar hoto a

Turkiya SPOR TOTO SUPER LİG wasannin mako na 14

 • 12:30 Osmanlispor vs Kasimpasa SK
 • 3:00 Konyaspor vs Antalyaspor
 • 6:00 Kayserispor vs Besiktas

Scotland Premier League wasannin mako na 17

 • 1:30 Dundee F C vs Aberdeen
 • 4:00 Ross County vs St. Johnstone
 • 4:00 Kilmarnock vs Dundee United FC

Girka Superleague wasannin mako na 13

 • 2:00 Asteras Tripolis FC vs Iraklis
 • 4:15 Xanthi vs Platanias
 • 6:30 Panthrakikos FC Komotini vs Olympiacos
Hakkin mallakar hoto Reuters

12:25 Spanish League Primera wasannin mako na 14

 • 4:00 Real Madrid CF vs Getafe CF
 • 6:15 Granada CF vs Atletico de Madrid
 • 8:30 Valencia C.F vs FC Barcelona
 • 10:00 Deportivo La Coruna vs Sevilla FC
 • 10:05 Real Betis vs Celta de Vigo
Hakkin mallakar hoto Getty

Italian Calcio League Serie A wasannin mako na 15

 • 3:00 Torino FC vs AS Roma
 • 8:45 Internazionale vs Genoa
Hakkin mallakar hoto Reuters

German Bundesliga wasannin mako 15

 • 3:30 Borussia Monchengladbach vs Bayern Munich
 • 3:30 Hamburger SV vs FSV Mainz 05
 • 3:30 FC Koln vs FC Augsburg
 • 3:30 Hertha Berlin vs Bayer 04 Leverkusen
 • 3:30 FC Ingolstadt 04 vs TSG Hoffenheim
 • 6:30 VfL Wolfsburg vs BV
Hakkin mallakar hoto AFP

French League wasannin mako 17

 • 5:00 Olympique Lyonnais vs Angers
 • 8:00 GFC Ajaccio vs Nantes
 • 8:00 Bastia vs AS Monaco FC
 • 8:00 Caen vs Lille OSC
 • 8:00 Stade de Reims vs ES Troyes AC
 • 8:00 Toulouse FC vs Lorient

12:10 A shirinmu na sharhi da bayannan gasar Premier Ingila.

Hakkin mallakar hoto Reuters

wannan mako za mu kawo muku wasan sati na 15 a karawar da za a yi tsakanin Arsenal da Sunderland, za mu fara gabatar da shirin da karfe 3:30 agogon Nigeria da Nijar. Kuna da damar tafka muhawara kan fafatawar da sauran wasannin Premier da za a yi a dandalinmu na muhawara da sada zumunta a BBC Hausa Facebook ko kuma a BBC Google +.

12:05 Gasar English Premier League wasannin mako na 15

 • 1:45 Stoke City FC vs Manchester City
 • 4:00 Southampton FC vs Aston Villa
 • 4:00 Swansea City vs Leicester City
 • 4:00 Arsenal FC vs Sunderland
 • 4:00 Watford vs Norwich City
 • 4:00 West Bromwich Albion FC vs Tottenham Hotspur
 • 4:00 Manchester United vs West Ham United
 • 6:30 Chelsea FC vs Bournemouth FC