An ci Bayern Munich a karon farko a Bundesliga

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Bayern Munich tana nan a matakinta na daya a kan teburi

Borussia Monchengladbach ta doke Bayern Munich da ci 3-1 a gasar Bundesligar Jamus da suka fafata a ranar Asabar.

Sai da aka dawo daga hutun rabin lokaci ne Borussia Monchengladbach ta ci kwallayenta uku ta hannun Oscar Wendt da Lars Strindl da kuma Fabian Johnson.

Frank Ribery wanda ya dawo daga jinyar raunin da ya yi watanni tara ne ya zare kwallo daya saura minti tara a tashi daga wasan.

Wannan shi ne karon farko da aka doke Munich a gasar Bundesliga bana, bayan da ta buga wasanni 15.

Har yanzu Bayern Munich tana mataki na daya a kan teburi da maki 40, Bor. Dortmund wacce ta yi wasanni 14 ke biye a mataki na biyu da maki 32, B M'gladbach ta uku da maki 26.