Habu Na Dutsen Mari ya doke Shagon Mada

Image caption A turmin farko Habu na dutse Mari ya doke Shagon Mada

Habu na Dutsen Mari ya doke Shagon Mada a turmin farko a dambatawar da suka yi a gidan damben Ali Zuma dake Dei-Dei a Abuja, Nigeria da safiyar Lahadi.

Tun da farko Shagon Mada da Shagon Na Manu zai dambata, wanda a kuma lokacin ne Habu ya so ya buga dambe da Mai Takwasara.

Yan kallo kuma sun bukaci ganin fafatawa tsakanin Habu da Mai Takwasara, amma Shagon Mada ya bukaci da sai ya dambata da Habun, kuma hakan suka amince da su kara a tsakaninsu.

Ga sauran wasannin da aka buga ba tare da an yi kisa ba:

  1. Matawallen Kwarkwada daga Kudu da Shagon Bahagon Musan Kaduna daga Arewa
  2. Dan Basiru daga Kudu da Alin Tarara daga Arewa
  3. Shagon Lawwalin Gusau daga Arewa da Dan Garkuwan Autan Faya daga Kudu
  4. Autan Faya daga Kudu da Bahagon Audu Argungu daga Arewa
  5. Cika dan Guramada da Aleka daga Kudu
  6. Garkuwan Shagon Mada daga Kudu da Fijot daga Arewa.