Mai goyon bayan Valencia ya mutu a wasa da Barcelona

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Neville zai jagoranci Valencia zuwa karshen kakar bana

Valencia ta ce wani magoyin bayanta ya mutu a lokacin da take yin wasa da Barcelona a gasar La Liga a filinta na Mestalla a ranar Asabar.

Rahotanni na cewa magoyin bayan ya mutu ne a lokacin da yake yin murnar farke kwallon da Barcelona ta ci Valencia a karawar da suka tashi kunnen doki 1-1.

Wasan da Valencia ta buga shi ne na farko tun lokacin da ta sanar da nada tsohon dan kwallon Manchester United da Ingila Gary Neville a matsayin kociyan kungiyar.

Kuma fafatawa ta biyu kenan da kungiyar ta buga canjaras daga wasanni uku da ta yi a jere a gasar ta La Liga.

Bayan da aka tashi daga wasa ne Valencia ta fitar da wata sanarwar tana bakin ciki da jin labarin mutuwar magoyin bayan nata a lokacin da take yin wasa a ranar Asabar.