"Da kyar idan Chelsea za ta kare a 4 farko a Premier"

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mourinho ya ce Chelsea ba za ta fadi daga gasar Premier ba

Jose Mourinho ya ce da kyar ne idan Chelsea za ta iya samun gurbin shiga gasar cin kofin zakarun Turai a badi.

Kocin na nufin da wuya idan Chelsea za ta iya kare gasar Premier bana a cikin sahun kungiyoyi hudun farko da za su sami gurbin shiga gasar cin kofin zakarun Turan.

Mourinho ya fadi hakan ne bayan da Bournemouth ta ci Chelsea 1-0 a Stamford Bridge a gasar Premier wasan mako na 15 da suka kara a ranar Asabar.

Ya kuma ce "Tun kafin su buga da Bournemouth suna tunanin yadda za su bar matsayin da suke kai a gasar, amma yanzu suna tunanin yadda za su kare a cikin shidan farko ne."

Wannan ne karo na takwas da aka doke Chelsea a gasar ta Premier, bayan wasanni 15 da ta buga, inda ta ci fafatawa 4 ta kuma buga canjaras a wasanni uku.